Jerin Kasashen da su ka fi karancin jama’a a Duniya
Mun leka sauran bangarori na Duniya inda mu ka kawo maku jerin kasashen da ba su da yawan al’umma. Daga ciki dai akwai kasar Vatican wanda ana kiyasin cewa mutanen cikin ta ba su kai 1, 000 ba.
Ga dai jerin kasashen na kamar haka:
1. Vatican City
Mutanen Kasar Vatican dai in sun yi yawa shi ne su kai 1000 kamar yadda bincike ya nuna a bara. Kasar ta Vatican can dai ba ta da girma kuma a nan ne Fafaroma na Kiristocin Duniya yake zama.
KU KARANTA: Labarin wani gari da ba a sata a Duniya
2. Tuvalu
Kasar Tuvalu ce ke bin bayan Vatican wajen karancin Jama’a. A 2016 Kasar ta Tuvalu da ke Yankin Nahiyar Oceania na da mutane ne da ba su kai 12, 000 ba kamar yadda binciken Bankin Duniya ya nuna.
3. Palau
Kasar Palau wanda ke Nahiyar Oceania kamar Tuvalu dai kasa ce maras jama’a. Babban bankin Duniya tayi bincike a 2016 inda ta bayyana cewa gaba daya mutanen kasar 20, 000 da nema kacal.
Kwanaki kun ji cewa Najeriya dai ta samu shiga cikin sahun farko na kasashen da ke da hadarin zama ga mata a shekarar nan ta 2018 da ake ciki. Kasar da ta zo kan gaba a wannan jeri ita ce Indiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng