Fulani makiyaya sun ci wasu Inyamurai taran naira miliyan 2 saboda kashe musu shanu
Saura kiris da labari ya sha banban a wani kauye dake cikin karamar hukumar Udi na jihar Enugu, biyo bayan karkashe shanun Fulani makiyaya da wasu matasan kabilar Ibo suka yi, wanda hakan ya harzuka makiyayan, amma dai an samu sulhu.
Jaridar The Sun ta ruwaito shugaban al’ummar yankin, Kelvin Ochi ne ya tabbatar da wannan labari, inda yace a sakamakon wannan barna da matasan Ibo suka yi ma Fulani, Fulanin sun nemi a biyasu naira miliyan biyu, inda yace a yanzu haka sun sauke musu naira dubu dari shida.
KU KARANTA: Hirde: Miyetti Allah ta yanke hukuncin daukan mataki kan al’adar badala
“Makiyayan sun shigo kauyenmu ne, inda suka kama ma wasu matasa akan zargin wai sun kashe musu dabbobi, inda suka yanke mana naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa, zuwa yanzu dai mun basu naira dubu dari shida.” Inji shi.
Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Ochi yana kokawa kan barnar da yace suma shanun Fulani suke yi ma manoman kauyen ta hanyar cinye musu amfanin gona, tare da yi ma matansu fyade, da kuma kashe musu jama’a.
Ochi yace ko a kwanakin baya sai da makiyayan suka harbi wani karamin yaro mai shekaru 13, wanda a yanzu haka yana nan kwance a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Enugu, ya kara da cewa al’ummarsa sun tsere daga garuruwansu saboda ayyukan makiyaya, kuma yace kwamitin zaman lafiya na gwamnatin jihar baya sauraron kukansu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng