Nigerian news All categories All tags
Kotu ta hana Dasuki bukatar da ya nema na a biya shi N5bn na barnar da aka yi masa

Kotu ta hana Dasuki bukatar da ya nema na a biya shi N5bn na barnar da aka yi masa

Wata babban kotun tarayya dake Abuja ta hana a biya tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki naira biliyan 5 da ya nemi a biya shi kan ci gaba da tsare shi da hukumar DSS suka yi.

Channels TV ta rahoto cewa a zaman kotu da akayi a ranar 2 ga watan Yuli, Dasuki ya bukaci a basa naira biliyan 5 na barna sannan kuma ya nemi a umurci hukumar DSS da babban alkalin tarayya da su bashi hakuri a bainar jama’a kan cigaba da tsare shi da suka yi ba bisa ka’ida ba.

Kotu ta hana Dasuki bukatar da ya nema na a biya shi N5bn na barnar da aka yi masa

Kotu ta hana Dasuki bukatar da ya nema na a biya shi N5bn na barnar da aka yi masa

Kotun ta hana a biya kudin damejin sannan ta ce lallai hukumar DSS ta shirya tattaunawa da Kanal Sambo Dasuki anan gaba batare da tsare shi ba a ranar aiki.

KU KARANTA KUMA: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Katagum

Justis Ijeoma Ojukwu ta bayar da belin Dasuki akan kudi naira miliyan 200 ta kuma jadadda cewa an bayar da belin sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel