Shugaban kasar Gambiya ya cire Mataimakiyar sa
Wannan shine karo na farko da shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya yiwa gwamnatinsa kwaskwarima, inda ya cire mataimakiyar sa da kuma wasu manyan ministocin sa guda uku
Wannan shine karo na farko da shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya yiwa gwamnatinsa kwaskwarima, inda ya cire mataimakiyar sa da kuma wasu manyan ministocin sa guda uku.
Shugaba Barrow ya cire mataimakiyar tasa Fatoumata Jallow da ministan sa na harkokin waje Ousainou Darboe.
DUBA WANNAN: Ta hada baki da mahaifiyarta sun kashe mahaifinta
A sanarwar da kafafen yada labarai suka fitar, sun nuna cewa an baiwa Jallow mukami na aiki a kasar waje amma har ya zuwa yanzu bata bayyanawa jama'a wane irin aiki bane.
Darboe kuma shine shugaban jam'iyyar Barrow a jam'iyyar UDP, wanda bayan an daure shi na shekara 3 sai Barrow ya zama shugaban jam'iyyar.
Sannan Barrow ya kori Ministan sa na ayyukan Gona Umar Jallow wanda ake zargi da aikata cin hanci da rashawa.
Bayan haka kuma ya kori Ministan Matasa Henry Gomez da kuma Ministan Sadarwa Demba, wadanda ake zargin basu kware akan aiki nasu ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng