Mutanen da su ke shirin fitowa takarar Shugaban kasa daga Arewawacin Najeriya

Mutanen da su ke shirin fitowa takarar Shugaban kasa daga Arewawacin Najeriya

Yanzu haka dai kusan an buga gangar siyasar 2019 inda ake shirin zaben shugaban kasa. Kwanan nan ne ma dai mu ka ji cewa tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna cewa zai doke Shugaba Buhari idan yayi takara.

Mutanen da su ke shirin fitowa takarar Shugaban kasa daga Arewawacin Najeriya
Attahiru Dalhatu Bafarawa ya fito takarar Shugaban kasa

Kawo yanzu dai akwai wasu ‘Yan siyasan da ba a san da su ba sosai da su ke shirin yin takara a 2019.

1. Attahiru Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya tabbatar da cewa zai yi takarar Shugaban kasa a 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP. Bafarawa yace shi ya fara kawo Shugaba Buhari siyasa kuma an dade ana damawa da shi.

KU KARANTA: Kwankwaso ya bayyana yadda za a doke Shugaba Buhari

2. Kabiru Tanimu

Tsohon Ministan Kasar nan a lokacin PDP Kabiru Tanimu Turaki SAN ya fito takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawar. Yanzu ma dai tsohon Ministan ya fara baza fastocin takara a Garuruwa na Arewacin kasar.

3. Yusuf Datti Ahmed

Sanata Yusuf Datti ya tabbatar da cewa zai yi takarar Shugaban kasa a karkashin babban Jam’iyyar adawar kasar. Datti Yusuf ya taba lashe kujerar Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar CPC a 2011 kafin Kotu ta karbe kujerar.

Bayan nan dai akwai manyan ‘Yan siyasar kasar da ke harin kujerar Shugaban kasa a PDP irin su Atiku Abubakar, Sule Lamido Ahmed Makarfi, Ibrahim Hassan Dankwambo da kuma watakila Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng