Abinda ya kamata kuyi idan har kuna son kama Shekau cikin ruwan sanyi – Kwamandan Boko Haram ga Sojoji

Abinda ya kamata kuyi idan har kuna son kama Shekau cikin ruwan sanyi – Kwamandan Boko Haram ga Sojoji

Wani tubabben kwamandan Boko Haram, Rawana Goni ya tabbatar ma rundunar Sojin Najeriya cewa shi kadai zai iya sanya shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau mika wuya tare cikin ruwan sanyi, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Goni ya bayyana mata haka ne a wani sansanin warware akidar Boko Haram na tubabbun yayan kungiyar dake garin Maiduguri, inda yace baya ga Shekau, zai iya gayyatar manyan kwamandoji guda 137 suma su mika wuya.

KU KARANTA: Wani Kwarto da kwartuwarsa sun fuskanci tsatstsauran hukunci a Jigawa

Shi dai Goni ya mika wuya ga Sojoji ne a kasar Kamaru tun kimanin watanni takwas da suka gabata, bayan ya tsere daga dajin Sambisa, inda yace ya rike mukamai da dama a kungiyar, na karshe shi ne shugaban yin sulhu a tsakanin mayakan.

Abinda ya kamata kuyi idan har kuna son kama Shekau cikin ruwan sanyi – Kwamandan Boko Haram ga Sojoji
Kwamanda

“Na ceci mutane da dama da aka yanke musu hukuncin kisa, kuma na yi sanadin saukaka hukunci akan wadanda suka aikata laifuka daban daban, inda daya daga cikin masu mutunci a kungiyar, kuma suna jin maganata.

“Na shiga Boko Haram kimanin shekaru biyar da suka gabata, bayan wani hari da yan ta’addan suka kai garinmu a Bama, daga nan na tsere da iyalina zuwa kasar Kamaru, inda anan ma suka iske ni, sai na fahimci babu yadda zan iya cigaba da rayuwa ba tare da na bi su ba, da haka na shiga,

“Bayan yan kwanaki da shigata, muka bude wani sansanin bada horo a kan iyakar kasar Kamaru da Najeriya, wanda muka sanya ma suna Aluska, mun kai harinmu na farko bayan kammala samun horo zuwa wani shingen Sojoji a Kamaru, inda muka kashesu, muka dauke makamansu, wannan abu ya faranta ma Shekau rai ace mu biyar mun yi wannan aiki, anan ya nada ni kwamada.

“Daga bisani kuma na fara diban sabbin mayaka, dayake ana so kwamdan yana da akalla mayaka guda 250 a karkashinsa, da haka muka dinga kai hare hare a Waza, Damaga, Banki, har ma da garina, Bama. Daga nan ne na fara tausaya ma mutanen da rikicin nan ya rutsa dasu, da haka kuma na fara kokarin sakosu, inda na sako mutane sama da 300.” Inji shi.

Dayake tsokaci kan Shekau kuwa, cewa ya yi lafiyarsa kalau, babu abinda ya same shi, yace ya taba karyewa shekaru biyar da suka gabata ta hanyar fadowa daga bisa Doki, toh amma ya warke, anan ne ya nemi Sojoji su bashi dama ya kirasa a waya, tare da mayakansa guda 137, dukkansu zasu mika wuya ciki ruwan sanyi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel