Kurunkus: Sabuwar nPDP da APC zasu cimma matsaya a wannan makon

Kurunkus: Sabuwar nPDP da APC zasu cimma matsaya a wannan makon

- A cikin makon nan 'yan sabuwar nPDP za su tabbatar da matsayarsu

- Dangantaka dai ta dade da yin tsami kan yadda 'yan sabuwar nPDP suke korafin ana musu wariya

Mammabobin Jamiyyar PDP da su ka shiga cikin Jamiyyar APC a kakar zaben Shekarar 2015 Masu lakabin nPDP sun ce za su bayyana matsayarsu akan zamansu a cikin Jamiyyar APC a cikin makon nan.

Kurunkus: Sabuwar nPDP da APC zasu cimma matsaya a wannan makon
Kurunkus: Sabuwar nPDP da APC zasu cimma matsaya a wannan makon

Mambobin wadanda su ka hadar da Alhaji Abubakar Kawu Baraje, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, kakakin Majalisar dokoki, Yakubu Dogara Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal da sauransu.

KU KARANTA: An kama wata babbar jigo a APC tana safarar mata zuwa turai

Shugaban ‘yan sabuwar PDP din ne ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ofishinsa na hulda da kafafen yada labarai da ke garin Ilorin a jihar Kwara, a jiya Lahadin.

Ya bayyana cewa Bayan kammala tuntuba da shawarwari za su yanke hukuncin kafin karshen makon nan. ya kara da cewa hukuncin zai tabbatar da cigaban ‘yan kasar nan.

Sannan ya bayyana cewa mutunta ra'ayin yan kasar nan da kuma hadin kansu shi ne abin da su ka sanya a gaba.

A karshe ya godewa ‘yan Najeriya bisa irin goyon bayan da su ke ba su akan gwagwarmayar da su ke, musamman kafafen yada labarai da su ke bibiyar al'amuransu sau da kafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng