Kungiyar makiyaya ta magantu a kan rikicin Filato, ta bayyana kabilar dake da laifi

Kungiyar makiyaya ta magantu a kan rikicin Filato, ta bayyana kabilar dake da laifi

Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah na yankin kudu maso gabacin Najeriya, Gidado Siddiki ya nisanta kungiyar da kashe-kashen rayyuka da akayi a wasu garuruwa jihar Filato.

A wata sanarwa da ya fitar a madadin 'ya'yan kungiyar a jiya a garin Awka ta jihar Anambra, Siddiki ya yi ikirarin cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa 'yan bindigan kabilar Berom ne suka saka shinge a titunan garin kuma suka rika kashe mutanen da suka ganin makiyansu ne.

Kungiyar makiyaya ta magantu a kan rikicin Filato, ta bayyana kabilar dake da laifi

Kungiyar makiyaya ta magantu a kan rikicin Filato, ta bayyana kabilar dake da laifi

KU KARANTA: Shugaban 'yan daban Sakkwato ya shiga hannun hukuma

A cewarsa, kadidiga ya nuna cewa daga shekarar 2016 kawo yau, 'ya'yan kungiyar sun rasa mutane 500 a jihohin Filato da Taraba da Benue a hanyarsu ta komawa Arewa ko kuma zuwa Kudu maso gabashin kasar.

Sai dai ya yi kirar a zauna lafiya tsakanin makiyaya Fulani da mutanen garuruwan da suke zaune saboda rikici baya haifar da wani abin alkhairi.

Ya kuma shawarci mahukunta a Najeriya su tabbatar sun hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin kashe-kashe ba tare da la'akari da kabilar ko addini ko gari ba.

Ya ce ta haka ne kawai gwamnatin zata iya samar da tsaro ga al'ummar kasar baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel