An kashe wani jigon jam'iyyar APC a kasar nan
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Imo ta fada cikin wani tashin hankali, bayan kashe wani jigo da wasu mutane da har yanzu ba a san su waye ba suka yi, mutumin wanda aka bayyana sunan sa da Mista Amos Akano
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Imo ta fada cikin wani tashin hankali, bayan kashe wani jigo da wasu mutane da har yanzu ba a san su waye ba suka yi, mutumin wanda aka bayyana sunan sa da Mista Amos Akano.
DUBA WANNAN: DSS sunyi babban kamu a jihar Anambra
Akano ya taba yin Darakta janar na Ezihe Foundation, daya daga cikin kungiyar da suke goyon bayan shugaban ma'aikatan jihar a karkashin gwamnan jihar Rochas Okorocha, Mista Uche Nwosu.
A yanda wani mutum ya bayyana, Martins Nwadike, wanda ya bayyanawa majiyar mu kisan, ranar Alhamis dinnan, yace da farko an fara sace mutumin ne jim kadan bayan sun kammala taron jam'iyya na jihar. Inda ya kama hanyar shi zuwa gida (Nkwerre) daga garin Owerri babban birnin jihar, 'yan bindigar sun tsare shi akan hanyar Isu - Njaba, suka wuce dashi.
Nwadike yace "yan bindigar sun gudu dashi, inda daga baya sai gawar shi muka gani.
"Muna bukatar hukumar tsaro dasu dauki mataki kwakkwara akan wannan lamari, ba a san jihar Imo da rikice - rikice ba. Wadanda suke kashe wasu domin samun mulki a hankali asirin su zai tonu kuma zasu ji kunya nan bada dadewa ba.
Har ya zuwa yanzu dai jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sabda Mr. Andrew Enwerem, bai ce komai akan lamarin ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng