Ta kashe mijinta saboda yace zai yi mata kishiya
Wata mata wacce aka bayyana sunanta da Salamatu Shehu ta yi sanadiyyar kashe mijinta a kauyen Rafin Gero dake karamar hukumar Anka a jihar Zamfara
Wata mata wacce aka bayyana sunanta da Salamatu Shehu ta yi sanadiyyar kashe mijinta a kauyen Rafin Gero dake karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.
DUBA WANNAN: An harbi wani yaron dan takarar gwamna
Kisan ya samo asali ne bayan fada ya rincabe a tsakanin mata da mijin, bayan da mijin ya nuna ra'ayin shi na sake aure, majiyar mu Legit.ng ta samu rahoton cewar, mijin ya yanke hukuncin rabuwa da tsohuwar matar tashi bayan, inda ya nuna ya gaji da irin zaman da yake yi da ita. A lokacin Salamatu ta dauki kujera ta bugawa mijin nata inda ya kwanta warwas baya motsi. Anyi gaggawar garzayawa dashi asibiti, inda daga baya yace ga garin ku nan.
Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewar yanzu haka matar tana hannu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng