An harbi wani yaron dan takarar gwamna

An harbi wani yaron dan takarar gwamna

A ranar Larabar nan ne data gabata wasu 'yan bindiga dadi suka harbi Salisu Tanimu, mataimaki a gurin dan takarar gwamnan jihar Nasarawa a karkashin jam'iyyar APC, Ahmed Aliyu Wadada, a karamar hukumar Keffi dake jihar Nasarawa

An harbi wani yaron dan takarar gwamna
An harbi wani yaron dan takarar gwamna

A ranar Larabar nan ne data gabata wasu 'yan bindiga dadi suka harbi Salisu Tanimu, mataimaki a gurin dan takarar gwamnan jihar Nasarawa a karkashin jam'iyyar APC, Ahmed Aliyu Wadada, a karamar hukumar Keffi dake jihar Nasarawa.

DUBA WANNAN: Shari'a sabanin hankali: sun saci abin dubu 20 an caje su dubu 300

An yiwa Atiku mummunan rauni a bayan shi, bayan 'yan bindigan sun tare motar shi a babbar kofar shiga jami'ar jiha dake garin Keffi da misalin karfe 9:30 na dare.

Wani dan uwan wanda abin ya shafa, Yakubu Shehu, ya sanarwa majiyar mu Legit.ng a jiya, inda yake cewa 'yan bindigar sun tursasa Atiku fitowa daga motar sa, suka kwace wayoyin sa na hannu, da kudi sannan suka harbe shi a baya, suka tafi suka barshi a wurin a kwance a kasa, suka kuma tafi da motar shi. Daga baya aka yi gaggawar garzayawa dashi asibiti, inda a yanzu haka yana karbar magani kuma yana samun sauki.

Hon. Ahmed Wadada yace shi baida masaniya akan kai wa yaron nashi hari da 'yan bindigar suka yi, amma dai an mikawa hukumar 'yan sanda rahoton komai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng