Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Togo

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Togo

-Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar katsina

- Ya tafi jajintawan gwamnati da mutan jihar kan annobar da ya afka musu

- Jihar Katsina ce jiha ta 3 da Buhari ya ziyarta domin jaje a makon nan

Saukansa a jihar Katsina ke da wuya, Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe, a gidan gwamnatin jihar Katsina a yau Juma'a, 29 ga watan Yuni, 2018.

Shugabannin kasashen biyu sun tattauna ne kan yadda za'a karfafa alakar diflomasiyya tsakaninsu. Kasar Togo dai na daga cikin kasashen Afrika ta yamma kuma mambar kungiyar tattalin arzikin Afrika ta yamma wato ECOWAS ce.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Togo

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Togo

Bayan ganawarsa da shugaban kasan Togo, shugaba Muhammadu Buhari ya tafi birnin Nouakchott, kasar Mauritania domin halartan taron gamayyar kasashen Afrika na 31 da za’ayi ranan 1 da 2 ga watan Yuli, 2018.

KU KARANTA: Hotunan kyakkyawan tarban da Buhari ya samu yau a Katsina

Taron na wannan shekaran dai na ke take : “Samun nasara kan yaki da rashawa: Yadda za’a kawo sauyi nahiyar Afrika”. kuma Shugaba Muhammadu Buhari ne zai gabatar da jawabi na musamman akan wannan take.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel