Buhari zai yi bincike: Cikin shuwagabannin hukumar kwallon kafan Najeriya ya duri ruwa
Karfafan alamu sun bayyana dake nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirin fara gudanar da binciken kwakwaf akan shuwagabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, biyo bayan bindigar da suka dinga yi da kudade a gasar cin kofin Duniya, ba tare da samun sakamakon mai kyau ba, inji rahoton jaridar Guardian.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles ta gagara tabuka wani abin kirki a wannan gasa dake gudana a kasar Rasha, inda kasar Ajantina ta sallamota daga rukunin D a ranar Talata.
KU KARANTA:
Wani babban jami’I daga ma’aikatar wasanni ya shaida ma majiyarmu cewa shugaba Buhari bai ji dadin irin labaran da yake samu ba daga sansanin yan Najeriya dake Rasha, inda yace Buhari ya umarci Minista Dalung ya duba lamarin da idon basira.
“Dama can Minista Dalung ya tsimayi hakan zai iya faruwa, don haka ya shawarci NFF su san adadin mutanen da zasu tafi dasu Rasha, yanzu ga irinta nan, suna da bindiga da kudi, har Buhari ya sa Minista ya bincikesu, ya kai masa rahoto.” Inji shi.
A wani labari kuma, shugaban NFF, Amaju Pinnick ya fara farautar tikitin zarcewa akan mukaminsa karo na biyu, ido rufe, inda ya aka ruwaito ya mika ma sakataren NFF, Muhammed Sunusi katin cire kudinsa don ya biya kudin dakin kwanansu da ya kai dala dubu Talatin.
“Wannan ya wuce iyakar fidda kudi da doka ta tanadar, don haka za’a iya yin amfani da shi akansa a gaban Kotu, musamman yanzu dayake ba shi da farin jini a wajen shuwagabannin hukumar, da kuma shuwagabannin kwamitin gudanarwa.” Inji wani na kusa da shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng