Sarki ya karrama yaron da ya haddace cikakken Al-Qur'ani a shekara 3
Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya bayar da lambar yabo ga wani dan yaro, Muhammad Shamsudeen, bisa hadar Al-Qur’ani mai girma da yayi a shekaru uku.
Daily Trust ta ruwaito cewa Muhammad, wanda ya kasance a aji na biyu a makarantar Naziri a Zari’a, jihar Kaduna, a 2016 ya haddace Qur’ani yana da shekaru uku wanda hakan ya bashi damar shiga gasar kasa da kasa a Saudiyya inda ya zo na biyu.
Legit.ng ta tattaro cewa a yanzu Muhammad na da shekaru biyar a duniya.
Da yake gabatar da lambar yabo ga yaron a fadarsa dake Zaria kwanan nan, sarkin wanda yayi Magana ta hannun daya daga cikin hadimansa, Alhaji Shehu Garba ya fadama ahlin Shamsudeen da masu masa fatan alkhairi cewa masarautarsa zata ci gaba da karrama wanda ya kamata.
KU KARANTA KUMA: Sule Lamido ya kayar da gwamnatin jihar Jigawa a kotu
Basaraken ya yabama iyayen yaron da makarantar bisa wannan kokari da kuma yuadda yaron ya wakilci Najeriya a gasar ta duniya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng