Gwamna Abubakar zai fito a shirin fim da Rahama Sadau ta fito a matsayin jaruma

Gwamna Abubakar zai fito a shirin fim da Rahama Sadau ta fito a matsayin jaruma

Labarin dake zuwa mana ya nuna cewa Gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Muhammed Abubakar, zai fito a cikin wani shirin fim da Rahama Sadau zata fito a matsayin jaruma.

Ana cigaba da daukar shirin mai taken "Up North" wanda zai fito cikin harshen turanci.

Kamar yadda wanda ya tsara labarin shirin, Editi Effiong, ya bayana gwamnan ya bada gudunmawa wajen shirya fim din.

A sakon da ya wallafa a shafin sa na Twitter, Effiong, ya sanar cewa gwamnan ya bayar da goyon baya wajen amfani da kambun daji na Yankari wurin hada shirin fim din kuma ya bada motocin sa yayin da ake neman motocin ayari domin maye wani matsayi na shirin.

Bayan haka, ya kuma bayyana cewa gwamnan ya amince da fitowa a wani matsayi na shirin bayan ya nema masu dama na daukar wani yanki na shirin a fadar sarkin Bauchi.

Gwamna Abubakar zai fito a shirin fim da Rahama Sadau ta fito a matsayin jaruma
Gwamna Abubakar zai fito a shirin fim da Rahama Sadau ta fito a matsayin jaruma

Majiyarmu a rahoto cewa Gwamnan ya ce dalilinsa na taimakawa wajen haska shirin shine saboda farfado da harkar kasuwanci a jihar Bauchi.

Yace tun ba yau yake neman masu shirya fim a Najeriya da su taho jihar domin shirya wasa.

Daga karshe gwamnan yana mai kyautata zato cewa, matsayin da ya dauka na fitowa a cikin shirin wasan kwaikwayo zai ba wa matasa karfin gwiwa wajen yin sana'ar ga masu sha'awar yin haka.

Shirin zai samu hasakawar fitattun yan wasan kamar, Rahama Sadau da TBoss, Banky W, Michelle Dede, Ibrahim Onimisi-Suleiman, Akin Lewis, Hilda Dokubo da Kanayo O Kanayo.

KU KARANTA KUMA: Sai da na fada wa Kwankwaso kada ya dora Ganduje, gashi yanzu yana dandana kudar sa – Hon Sumaila

Shirin wanda take bada labarin soyayya, siyasa da zamantakewa zai fito ga kasuwa cikin watan Disamba na bana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng