Dalilin da yasa kabilar Himba basa yin wanka
Namibia wata kayatacciyar kasa ce a kudancin Afirka. Kasar na dauke da tsaunika, kogi mai dauke da manyan kifaye, filin ciyawar kalahari da kuma namun daji. Wadannan abubuwan su suka kara kawatar da kasar Namibia
Namibia wata kayatacciyar kasa ce a kudancin Afirka. Kasar na dauke da tsaunika, kogi mai dauke da manyan kifaye, filin ciyawar kalahari da kuma namun daji. Wadannan abubuwan su suka kara kawatar da kasar Namibia.
Yaren Himba na kasar Namibia yanada al'adu daban daban. Ba al'adun su kadai yasa sukayi fice ba, harda yanayin rayuwar su, suturar su da tattalin arzikin su.
DUBA WANNAN: Dalilin da ya hana a cire Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Filato
Ana kiransu da Omuhimba ko Ovahimba, suna rayuwa a arewacin Namibia, a yankin Kunene.
Duk da Yaren Himba kan yi mu'amala da sauran yarikan, amma suna rayuwar su a ware domin gujewa gurbacewar al'adun su. Suna da karamci ga baki da ma wadanda basu sani ba. Amma Sam basa maraba ga duk wani abu da zai kawo barazana ga al'adun su.
Mutanen Yaren Himba manoma ne kuma makiyayan dabbobi irin su : akuyoyi, shanaye, tumakai da sauran su. Wasu daga cikin su nada addini.
Wani abun mamaki na mutanen shine basa wanka da ruwa. Zamu iya danganta wannan da yanayin garin. Suna da yanayin hamada mai tsanani kuma da rashin ruwa.
Rashin wankan su shine silar rashin tsaftar su. Yan Yaren suna shafa jar kasa a fatar su tare da yin surace a duk yammaci.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng