Gwamnatin Buhari ta sanar da ranar da za ta fara kashe kudaden Abacha da ta kwato

Gwamnatin Buhari ta sanar da ranar da za ta fara kashe kudaden Abacha da ta kwato

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewar za ta fara kashe kudaden da ta kwato daga cikin arzikin da tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya kai su kasashen waje daga watan gobe na Yuli.

Jaridar Punch ta ruwaito gwamnati ta ce zata kashe kudaden ne ta hanyar yi ma yan kasa hidima, kamar yadda mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tallafa ma jama’a, Maryam Uwais ta bayyana a ranar Alhamis,28 ga watan Yuni.

KU KARANTA:

Maryam ta bayyana haka ne a yayin taro da ofishin jakadancin kasar Switzerland dake Najeriya ta shirya ma jami’an gwamnatin Najeriya akan kudaden da kasar ta dawo ma Najeriyan, inda tace daga cikin sharadin da kasar Switzerland ya gindaya ma Najeriya shi ne, sai babban bankin duniya ya sanya idanu kan yadda gwamnatin Najeriya za ta kashe kudaden.

Gwamnatin Buhari ta sanar da ranar da za ta fara kashe kudaden Abacha da ta kwato
Abacha

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Maryam ta cigaba da cewa gwamnatin tarayya da wakilan babban bankin Duniya sun rattafa hannu kan yarjejeniya akan lallai Najeriya za ta kashe kudin akan yan kasa talakawa gajiyayyu.

“Kudaden da gwamnatin tarayya ke raba ma yan Najeriya gajiyayyu na naira dubu biyar biyar (N5000) ba daga kudin Abacha muke kashewa ba, amma zamu fara kashe kudin Abacha daga watan Yuli.” Inji Maryam.

Haka zalika, shugaban tsarin rabon kudi ga gajiyayyu na kasa, Dakta Temitope Sinkaiye yace zuwa yanzu jihohi guda goma sha takwasa, 18, da kuma yan gudun hijira dake sansanoni daban daban na jihar Borno suna amfana da wannan kudi, sa’annan ana ana horas dasu kan ayyukan sana’o’in hannu.

Daga cikin johohin dake amfana da wannan rabon kudi akwai Niger, Kogi, Ekiti, Oyo, Osun, Kwara, Cross River, Bauchi, Jigawa, Gombe, Benue, Taraba, Adamawa, Kano, Katsina, Kaduna, Nasarawa da Anambra. Inda yace sauran jihohi 18 basu fara cin gajiyar shirin ba saboda basu samar da ingantaccen yanayin hakan ba.

Shi ma jakadan kasar Switzerland, Eric Mayoraz yace a yanzu ajiyan kudin sata a kasarsu ya yi wahala sakamakon sauya dokokin ajiyan kudi a bankunan kasar, inda yace adadin kudin Abacha dake kasar ya kai dala miliyan 752 kuma sun dawo ma Najeriya su tun a shekarar 2005.

“Wadannan kudaden, dala miliyan 321 ba a kasae Switzerland suke ba, amma ministan shari’ar kasarmu ne ya daskarar da kudaden daga kasar da suke, kamar su Luxembourg.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel