Zamu dawwama a talauci muddin bamu rage haihuwa barkatai ba - Ministan Buhari
Ministan Kasuwanci da saka jari, Mr. Okechukwu Enelamah ya ce Najeriya za ta cigaba da dawwama cikin talauci muddin yan Najeriya basu dena haihuwan yara barkatai ba.
Ministan ya furta wannan magana ne a ranar Laraba yayin da ya ke tsokaci a kan rahoton Brookings da ta bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi yawan al'umma da ke fama da talauci a Najeriya.
"Ina tunanin ya kamata mu zage damtse a muyi aiki tukuru a matsayinmu na 'yan Najeriya, idan ba muyi hakan, mutanen mu za su cigaba da haihuwan yara barkatai kuma suna kara dilmiyewa cikin talauci," inji shi.
KU KARANTA: An cafke mutane biyu da ake zargi da tayar da bam a gidan tsohon Minista
"Ya kuma yi korafi a kan rahoton kasashen duniya mafi talauci da aka fitar cikin kwanakin nan inda ya ce cibiyar binciken da dauka alkallumanta ne lokacin da Najeriya ke cikin halin matsin tattalin arziki.
Majiyar Legit.ng ta fitar da rahoton cibiyar Brookings inda cibiyar ta bayyana cewa Najeriya tana gaba da kasar Indiya wajen adadin mutanen da ke fama ta talauci da fatara.
Mr. Enelamah ya ce: "Ya kamata mutane sun fahimci cewa lokacin da aka dauka alkaluman wannan rahoton, alkaluman Najeriya suna baya hakan na nufin cewa rahoton yana bayyana abin da ya faru a baya ne.
Duk da haka, Ministan ya ce akwai bukatar samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya cikin gagawa.
Ya yi kira ga al'umma su mayar da hankulansu wajen gudanar da ayyukansu saboda su taimakawa gwamnati wajen inganta rayuwar al'ummar kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng