Nigerian news All categories All tags
Rikicin Jos: Fadar Shugaban kasa ta bayyyana kokarin da Buhari ya ke yi

Rikicin Jos: Fadar Shugaban kasa ta bayyyana kokarin da Buhari ya ke yi

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana matakan da Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta dauka domin kawo karshen kashe-kashen da ya auku a Garin Jos inda mutane da dama su ka rasa ran su.

Ofishin PODE da ke fadar Shugaban kasa ta ayyano matakai 7 da Gwamnatin Tarayyar ta dauka daga lokacin da rikicin ya barke kawo yanzu.

Rikicin Jos: Fadar Shugaban kasa ta bayyyana kokarin da Buhari ya ke yi

Shugaba Buhari na kokarin kawo karshen rikicin Filato

Ga dai matakan nan kamar haka:

1. Sufeta na Sojin Najeriya ya aika Runduna ta musamman zuwa Garuruwan Barkin Ladi da kuma Kudancin Jos.

2. ‘Yan Sandan Najeriya sun aika Jiragen yawo zuwa Garuruwan Biyom da kuma sauran Kananan Hukumonin na Filato. Bayan nan kuma an tura makamai da sauran kayan aiki.

KU KARANTA: Gwamnan Filato ya caccaki masu zanga-zanga a Jos

3. Shugaba Buhari ya saki Naira Biliyan 10 domin biyan wadanda rikicin Benuwe, Nasarawa da kuma Filato ya auka da su.

4. Rundunar Sojojin Najeriya sun aika da Jami’ai na musamman ns Operation Safe Heaven zuwa inda abin ya shafa a Jihar Filato.

5. Bayan aukuwar abin ne Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya taka da kan sa ya tafi zuwa inda abin ya faru domin ganewa kan sa.

6. Washegari ne kuma Mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tashi ya tafi Jihar Filato domin kawo karshen rikicin.

7. Bayan nan ne kuma Shugaban Kasa Buhari ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara game da rikicin.

Kun san cewa dai rikicin Fulani da Birom a Garin Filato ya ci daruruwan mutane. Bincike ya nuna cewa kafin harin an kashe wasu Fulani a Yankin wanda hakan ya ja aka yi kisan gilla.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel