Shari’ar Maryam Sanda: An samu babban cikas, an sake daga zaman da watanni 3
Shari’ar Maryam Sanda, wacce ake zargi da kisan maigidanta, Bilyaminu Bello, ya samu cikas a yau Alhamis sakamakon rashin lafiyan lauyan gwamnati a kotu.
Yayinda aka dawo shari’ar a yau, lauyan gwamnatin CSP James Idachaba ya bukaci kotu ta daga karar saboda bai jin dadi kuma ba zai iya cigaba da zaman ba.
Yace: “Mai girma mai shari’a. ba ni jin dadi, ina bukatan ganin likti, da kyar na zo nan saboda muhimmancin wannan karar."
"Mai shaida da za’a yiwa tambayoyi na kotu yanzu domin nuna yadda muka dauki karar da muhimmanci, ina neman alfarman kotu ta daga wannan zama.”
Lauyoyin Maryam Sanda sun nuna amincewarsu da bukatar kuma saboda haka, Alkalin kotun, Jastis Yusuf Halilu, ya bada alfarman kuma ya daga karar.
Bias ga hutun alkalai da za’a je, an daga karar zuwa ranan 3 ga watan Oktoba bias ga yardan dukkan lauyoyin.
Gabanin yanzu, rahoto ya bayyana cewa lauyan Maryam Sanda, Joseph Daudu, ya bukaci kotu ta jinkirta masa domin wasu ayyuka da yake yi, amma daga isowarsa aka daga zaman.
KU KARANTA: Sarauniyar Ingila ba lafiya
Ana tuhumar Maryam Sanda da kisan mijinta, Bilyamin Bello, dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alh Bello Halliru Muhammad.
Tana gurfana ne tare da mahaifiyarta, Maimuna Aliyu; dan uwanta, Aliyu Sanda; da kuma wata Sadiya wacce ta taimaka wajen goge jinni mijin bayan kashe shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng