Rikicin Jos: Ya kamata Gwamnatin Tarayya da Jihar Filato su hada kai - Obasanjo

Rikicin Jos: Ya kamata Gwamnatin Tarayya da Jihar Filato su hada kai - Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya tofa albarkacin su game da rikicin Filato inda aka kashe mutane da dama a Garin Jos. Obasanjo yayi wa al’ummar Filato jajen abin da ya auku.

Olusegun Obasanjo ya nemi a kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a Kasar. Tsohon Shugaban Kasar ya bayyana wannan ne lokacin da ya kai ziyara wajen Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong a Garin Jos a jiya Laraba.

Rikicin Jos: Ya kamata Gwamnatin Tarayya da Jihar Filato su hada kai - Obasanjo
Obasanjo yayi kira a kawo karshen rikicin Jihar Filato

Obasanjo yace dole a hada kai a nemi mafita game da matsalolin da ake samu a kowane bangare da matakai na Gwamnati na Kasar. Tsohon Shugaban Kasar yace abin takaici ne ace a wannan zamani ana samun irin wannan kashe-kashe.

KU KARANTA: Kotu ta na neman tayi ram da tsohuwar Ministar Jonathan

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Tsohon Shugaban Kasar ya nemi a duba sababin wannan kashe-kashe a kuma dauki mataki. Obasanjo ya nemi Gwamnatin Tarayya da Jihar ta Filato su yi bakin kokarin su na kawo karshen rikicin.

Gwamnan Jihar Simon Lalong ya ji dadin ziyarar da Obasanjo ya kai inda ya nemi a zauna cikin kauna da soyaya da juna. Simon Lalong yace bayan hawan sa mulki yayi kokarin kawo karshen rikicin da ake yi tsakanin Fulani da ‘Yan kabilar Birom.

Kwanaki kun ji cewa Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun shiga Garin Filato domin kawo zaman lafiya bayan rikicin da ya barke a cikin Garin Barkin Ladi a karshen makon da ya wuce.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng