Gwamnatin Buhari na shirin cin wani bashin Dala Biliyan 2.8
Mun samu labari cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya na kokarin cin wani sabon bashi a wannan shekarar. Darekta Janar ta Ofishin kula da bashin Najeriya DMO Patience Oniha ta bayyana wannan.
Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari na kokarin cin bashin kudi daga bankunan Kasar waje a shekarar nan. Daga cikin Dala Biliyan 5.5 da Najeriya za ta ci bashi, Dala Biliyan 2.5 za su fito ne daga bankin Kasar waje.
KU KARANTA: Akwai hadari a zama a Najeriya - Bincike
Bayan nan kuma Patience Oniha ta bayyana cewa Najeriya za ta kashe Dala Biliyan $3 wajen biyan bashin da ake bin ta. A bara dai Najeriya ta bi a hankali wajen cin bashi domin gudun nauyi yayi wa a kasar yawa.
Shugaban DMO din watau Misis Patience Oniha ta tabbatar da cewa a shekarar 2017 dai Najeriya ta saida hannun jarin ta ne ta kuma tada kudi ta tsarin Sukuk domin bi a sannu da bashin da ake bin ta a gida da waje.
Bashin da ake bin Najeriya daga bankunan Kasar waje ya kai akalla kashi 23% na bashin da ke kan wuyar kasar. Ana ma tunani ruwan da Najeriya za ta biya zai karu saboda Kasar Amurka ta canza tsare-tsaren bashin ta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng