Yanzu Yanzu: An harbe tsohon dan takarar kujerar gwamna a Akwa Ibom har lahira
Wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba suka kashe shi a daren ranar Litinin, a otel dinsa dake Mowe jihar Ogun.
Victor Iyanam, tsohon alkalin alkalai a jihar Akwa Ibom sannan kuma ‘ya’ya ga marigayin dan siyasan kuma dan kasuwa ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa day a saki a ranar Alhamis da safe.
Marigayi Mista Iyanam ya tsaya takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar Accord Party a 2015 a jihar Akwa Ibom.
KU KARANTA KUMA: Tirsasa wa shugaban kasa aka yi ya saka hannu a kasafin kudin 2018 - Hadimin Buhari
Kafin fadawarsa a harkar siyasa ya yi aiki a matsayin babban darakta a gidauniyar Mike Adenuga’s Globacom Nig Ltd, Lagas.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng