Kisan Plateau: Masu zanga-zanga sun kai mamaya gidan gwamnati, sun lalata kayayyaki
Gwamnatin jihar Plateau ta bayyana cewa masu zanga-zanga akan kisan Barkin Ladi da yayi sanadiyan mutuwar mutane sama da 86 sun mamaye gidan gwamnati a ranar Laraba, 27 ga watan Yuni.
Rahoto sun sanar da cewa a zanga-zangar da suka yi sun lalata kayayyakin gwamnati na miliyoyin naira.
A wata sanarwa daga daraktan kula da harkokin labarai, Emmanuel Nanle, a daren ranar Laraba ya bayyana lamarin a matsayin abun kaico.
An tattaro cewa masu zanga-zangan sun sha kan jami’an tsaro a bakin kofar inda suka samu shiga sannan suka farfasa gilasan gine-ginen da motocin da aka ajiye a harabar gidan gwamnatin.
KU KARANTA KUMA: Tirsasa wa shugaban kasa aka yi ya saka hannu a kasafin kudin 2018 - Hadimin Buhari
An tattaro cewa masu zanga-zangan basu ga kokarin da gwamnati da jami’anta ke yi domin ganin an kawo mafita ga rikicin a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng