An gano wani sahihin maganin Cancer

An gano wani sahihin maganin Cancer

Wasu manyan masanan jami’ar kimiyya da fasaha da kuma ilimin kiwon lafiya ta garin Oregon dake kasar Amurka, sun tabbatar da cewar sun gano wani sahihin magani da zai iya kawar da nau’ika 4 na kwayoyin cutar daji

An gano wani sahihin maganin Cancer
An gano wani sahihin maganin Cancer

Wasu manyan masanan jami’ar kimiyya da fasaha da kuma ilimin kiwon lafiya ta garin Oregon dake kasar Amurka, sun tabbatar da cewar sun gano wani sahihin magani da zai iya kawar da nau’ika 4 na kwayoyin cutar daji.

DUBA WANNAN: Abubuwan da referee ya fadawa Mikel Obi jiya bayan an tashi wasa

Masu binciken sun samo wannan sabon magani mai suna KBU2046, wanda zai kawo karshen ciwon daji na mafitsara, nono, hunhu, da kuma hanji, inji wata mujalla mai suna ‘Nature Communications’.

A yayin wasu gwaje-gwaje da masanan suka yi akan wasu beraye, sun gano cewar maganin ya hana kwayoyin cutar dajin cigaba da yaduwa, sannan kuma ya dakatar da duk wata zirga-zirga da kwayoyin cutar suke a jikin berayen. inji babban likitan masu binciken Raymond Bergan.

A yanzu haka dai likitocin sun fara shirye-shiryen fara bawa mutane maganin mai suna KBU2046, domin kara tabbatar wa da duniya tasirin maganin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng