Nigerian news All categories All tags
Wasu fusatattun matasa sunyi wa gidan gwamnatin jihar Filato tsinke

Wasu fusatattun matasa sunyi wa gidan gwamnatin jihar Filato tsinke

Wasu fusatattun matasa dake kauyukan karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar filato sun yiwa gidan gwamnatin jihar Filato tsinke, inda suka dinga fasa kofofi da ababen hawa da suka samu a harabar gidan gwamnatin

Wasu fusatattun matasa sunyi wa gidan gwamnatin jihar Filato tsinke

Wasu fusatattun matasa sunyi wa gidan gwamnatin jihar Filato tsinke

Wasu fusatattun matasa dake kauyukan karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar filato sun yiwa gidan gwamnatin jihar Filato tsinke, inda suka dinga fasa kofofi da ababen hawa da suka samu a harabar gidan gwamnatin.

Majiyar mu Legit.ng tace, Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, ta jihar ce ta umarci duk mabiya addinin kirista dasu fita kwan su da kwarkwata domin gabatar da zanga zangar lumanar wadda ta kunshi maza da mata.

DUBA WANNAN: Baza mu sake zuwa aikin hajji ba - Limaman kasar Tunusiya

Masu zanga zangar sun hadu ne hanyar tsohon filin jirgin sama na garin Jos, inda suke sanye da bakaken kaya kuma rike da korayen ganye. A haka suka rankaya har gidan gwamnati.

A lokacin da masu zanga zangar suka isa gidan gwamnatin, Gwamna Simon Bako Lalong yaje raka Sanata Bukola Saraki asibitin koyarwa na jami'ar Jos, domin gaishe da wadanda suka samu rauni sakamakon harin.

A take masu zanga zangar suka fusata, inda suka farfasa gilasan kofofin gidan gwamnatin da kuma ginin shugabancin. Sun hada da motocin da suka gani a harabar gidan, wanda ya hada da motocin yan jarida.

Duk wani yunkurin da daraktan labarai da hulda da mutane na jihar, Samuel Emmanuel Nanle, yayi don tsayar dasu ya tashi a banza. Sai da jami'an tsaron wurin sukayi harbi a iska sannan suka watse.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel