Jami’an Yansandan Najeriya sun tarwatsa wani dandalin matsafa dake tsakiyar Daji (Hoto)

Jami’an Yansandan Najeriya sun tarwatsa wani dandalin matsafa dake tsakiyar Daji (Hoto)

Jami’an Yansandan Najeriya reshen jihar Legas sun kai farmaki wani sansanin matsafan kungiyar asiri ta OPC dake cikin wani Daji a kasar gadar Opebi, kamar yadda kwamishinan Yansandan jihar, Imohimi Edgal ya bayyana.

Jaridar Guardian ta ruwaito Edgak yana bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Yuni, yayin da ya jagoranci tawagar Yansanda zuwa sansanin matsafan, inda yace binciken su ya gano cewar ana azabtar da mutane a wannan wuri.

KU KARANTA: Atiku ya yi rabon miliyoyin nairori ga mutanen da ibtila’i ya fada musu a jihar Bauchi

Edgal ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewar sun kama mutane uku a wannan dandali na matsafa, yayin da suka gano na’urar cire kudade na POS guda uku, da kuma wayar hannu, katin cire kudi.

Jami’an Yansandan Najeriya sun tarwatsa wani dandalin matsafa dake tsakiyar Daji (Hoto)
Sansanin

“Mun samu rahoton wurin nan ne daga jami’an hukumar yan banga na jihar Legas, bayanin da muka samu ya sanya muka tura jami’in Dansanda mai mukamin DPO don yin sinitiri a yankin, inda aka hangi wasu mutane suna jan wani mutumi a kasa cikin dajin.

“Nan da nan Yansanda suka afka dajin, inda suka kama mutane uku, sa’annan aka ceto mutumin da ake kokarin yin tsafi da shi, sai kungiyar OPC abokan aikinmu ne a baya, amma ga shi nan wasu na amfani da sunansu suna yin barna.” Inji shi.

Wasu kanikawa dake aiki a kasan gadar sun bayyana cewa a bayyane kiri kiri matsafan ke cutar da duk mutumin da suka kama, inda suka kara da cewa har littafin laifi suke bude musu, inda suka tursasa ma mutane amsa laifin da ma basu yi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: