Yadda tsohon Gwamnan Niger ya biya 'yan kwangila na bogi N1.7bn
A ranar Talata, 26 ga watan Yuni ne aka ci gaba da sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu.
Hukumar EFCC dai na tuhumar tsohon gwamnan da aikata rashawa, inda ta gabatar da shaidar yadda y biya naira biliyan 1.7 na kudaden canjin yanayi gad an kwagila na bogi a shekarar 2014.
A yayinda yake bayar da shaida, Shugaban masu binciken asusu na jihar, Nmadu Ndawuya ya tabbatar wa kotun cewa gwamnatin tarayya ta baiwa jihar Naira Bilyan biyu na kudaden canjin yanayi inda aka baiwa ma'aikatan Muhalli Naira Bilyan 1.7 daga cikin kudaden.
Ya ci gaba da cewa a ranar da aka shigar da kudaden asusun ma'aikatar muhallin, an kuma zare su daga asusun, an biya wasu 'yan kwangiloli uku na bogi Naira Bilyan 1.7 wadanda ba a san su ba da kuma adireshin ofishisoshinsu ba.
KU KARANTA KUMA: Wani kyakyawan matashi ya auri mata biyu a rana daya ya karfafawa sauran maza gwiwar yin haka
Haka ma, EFCC ta gabatar da wani ma'aikacin Bankin " Eco Bank" mai suna, Waniko Ebenezer wanda shi ma, ya tabbatar da yadda aka biya wadannan kamfanoni uku kudaden.
A yau Laraba, 27 ga watan Yuni ne, za a ci gaba da sauraren karar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng