Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kauyukan Plateau ya tasar ma 100 – Yan sanda

Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kauyukan Plateau ya tasar ma 100 – Yan sanda

Rundunar yan sandan jihar Plateau sun bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kauyukan jihar ya tasar ma 100.

Kwamishinan yan sandan jihar, Undie Adie, ya bayyana hakan a lokacin wani hiran wayar tarho akan Channels TV a ranar Talata, 26 da watan Yuni.

Ya bayyana cewa rundunar yan sandan bata da masaniyar cewa irin wannan ta’asar zai afku, amma ta dauki mataki a take bayan ta samu labarin harin.

Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kauyukan Plateau ya tasar ma 100 – Yan sanda
Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kauyukan Plateau ya tasar ma 100 – Yan sanda

A halin da ake ciki, Shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara na cikin wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugabannin na ganawar ne akan kashe-kashe da aka yi a jihar Plateau a karshen makon da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Plateau: Mutane sun fara kaura daga gidajensu

Shugabannin majalisar dokokin Najeriya ne suka bukaci yin ganawar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng