Duba yadda wata daliba tare da masoyinta sun gamu da ajalinsu a lokaci guda

Duba yadda wata daliba tare da masoyinta sun gamu da ajalinsu a lokaci guda

- Kwanan wata daliba da saurayin ya kare ta wani yanayi mai ban mamaki

- Matasan sun mutu ne a cikin daki daya a rana daya

- Kuma har yanzu ba a kaiga gano musabbabin mutuwar tasu ba

Wata daliba yar ajin karshe mai karatu a jami'ar Imo dake jihar Imo mai suna Blessing Amam ta gamu da ajalinta a dakin Kwanan dalibai dake karamar hukumar Mbaitoli a jihar ta Imo.

Kafin rasuwarta dalibar dai ana sa ran zata kallama karatun ta ne a watan Agustan wannan shekara.

Duba yadda wata daliba tare da masoyinta sun gamu da ajalinsu a lokaci guda
Blessing Amam

Bayanai sun bayyana cewa Dalibar sun kwanta ne ita da masoyinta da zimmar tashi zuwa da safe amma bayan wayewar garin Litinin sai aka riske su rai ya yi halinsa.

Wata makociyar mai rasuwar ta bayyana cewa sai da suka fara jin wari ne sannan hankalinsu ya kai ga cewa warin na fitowa ne daga dakin Blessing wanda daga nan ne suka yi yunkurin ganin me ke faruwa.

KU KARANTA: Abin tausayi: Duba yadda wata uwa ta kwarawa danta kalanzir sannan ta cinna masa wuta

Ta ce "Bayan yara sun dawo daga makaranta ne sai suka fara jin wani mugun wari, da aka duba sosai sai aka gano daga dakin Blessing yake fitowa. A nan take wata kawarta ta kira wayarta amma shiru kake ji ba a amsa ba, nan dai aka samu aka balle kofar ta karfin tsiya kawai sai aka tsince su a mace baki dayansu.

kowanne kwance cikin jini da ya biyo ta baki da hancinsu kuma jikinsu duk ga alama nan kamar dukansu aka yi".

Wata majiya ta bayyanawa cewa a daren da abun zai faru dalibar bata dawo dakin kwanan dalibai da wuri ba sai cikin dare, amma duk da haka ba'a ji wani yanayi na fada ko tashin hankali a tsakanin masoyan ba.

Bayan da manema labarai suka ziyarci dakin Kwanan daliban sai suka iske babu kowa, ma'ana kowanne dalibi ya ranta a na kare saboda gudun kar jami'an tsaro su cafki mutum domin samun bayanai ko wani abu makamancin haka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng