Wani kyakyawan matashi ya auri mata biyu a rana daya ya karfafawa sauran maza gwiwar yin haka

Wani kyakyawan matashi ya auri mata biyu a rana daya ya karfafawa sauran maza gwiwar yin haka

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa wani matashi dan kasar Somaliya ya angwance da tsala-tsalan yan mata biyu a rana daya.

BBC ta rahoto cewa matashin ya ce ya aikata hakan ne domin ya karawa maza karfin gwiwar yin haka.

Saurayin mai suna Bashir Mohammed ya ce ya fara soyayya da 'yan matan biyu ne kimanin watanni takwas da suka gabata kafin su amince da bukatarsa ta aurensu.

Matashin ya jaddada cewa ya dade yana kawo yan matan gidansa a duk lokacin da suke tare domin su saba, sannan kuma ya ce yak an sanar das u yadda yake kaunarsu, sun kuma gamsu da hakan.

Wani kyakyawan matashi ya auri mata biyu a rana daya ya karfafawa sauran maza gwiwar yin haka
Wani kyakyawan matashi ya auri mata biyu a rana daya ya karfafawa sauran maza gwiwar yin haka

Matashin ya ce ya auri mata biyu ne tashi guda saboda yana "son yara da yawa".

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC

Gabilin al'ummar kasar Somaliya Musulmi ne wadanda addininsu ya amince musu su auri mace fiye da daya.

Sai dai ba a saba ganin saurayi ya auri mata biyu ba a rana daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng