Yansandan Najeriya sun yi jarumta wajen tartwatsa gugun yan fashi da makami
Rundunar Yansandan garin Warri na jihar Delta ta yi nasara damke wasu gaggan yan fashi da makami guda biyar da suka yi kaurin suna wajen satar motocin mutane a yankin garin Delta da kewaye.
Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito wata majiya ta karkashin kasa dake cikin rundunar ta bayyana mata haka a ranar Talata, 26 ga watan Yuni, inda yace guda daga cikin yan fashin ya mutu a hannun Yansanda.
KU KARANTA: Gasar cin kofin Duniya: Magen sa’a ta bayyana Najeriya za ta samu nasara akan Ajantina
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kama yan fashin ne a ranar 20 ga watan Yuni a rukunin gidaje na Bendel, bayan sun yi fashin wata babbar mota kirar Toyota Highlander a hannun wani mutumi a ranar 18 ga watan Yuni.
“Sun yar da motar a titin Eboh yayin da suka fahimci motar ta tsaya cak sakamakon wani na’urar kiyaye sata dake daure a cikin motar, ganin haka ya sa suka sauka, inda suka kara kwace wata mota kirar Toyota Corolla daga wajen wani mutum na daban.
“Bayan sun yi gajerar tafiya, sai motar ta samu matsala, anan ma suka sake kwace wata mota kirar Honda Pilot Jeep daga hannun wani direba, sai dai dubunsa ta cika a lokacin da suka ga yan banga, inda suka jefar da motar suka ruga, amma daga bisani sun shiga hannu” Inji shi.
Majiyar ya kara da cewa an gano kayan Sojoji da bindigu a hannunsu, sa’annan an gano motoci guda biyu da suka dauka, yayinda Yansanda ke cigaba da kokarin nemo guda daya da ta rage.
Su ma yan fashin sun amsa laifinsu, sa’annan sun bayyana cewar sun siya lambar mota ta gwamnatin jihar Delta akan kudi naira dubu dari, zuwa yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng