Da yiwuwar Argentina zata kori Messi idan basu ci Najeriya yau ba
- Messi na cikin tsaka mai wuya a wasan yau da zasu buga da Najeriya
- Idanun duk duniyar 'yan kwallo ya zuba a kansa
- Yau ce ranar da zai fitar da kasarsa kunya
Yau Talata ne da misalin karfe 7 :00pm na dare Nigeria zata buga wasanta na karshe na cikin rukuni da kasar Argentina a cigaba da gasar cin kofin duniya na 2018 da ake gudanarwa a kasar Russia.
Tsakanin Najeria da Argentina duk wanda ya ci wani shi ne zai samu damar tsallakawa rukuni na gaba, amma Najeriya ko da an tashi kunnan doki zata samu nasarar shallake siradin cikin rukunin, tuni dai kasar Croatia wadda take cikin rukuni na D tare da kungiyoyin biyu ta hada makinta shida bayan da ta samu nasara akan Najeriya da kuma Argentina.
Amma wani abu da yake shirin daukar idon ‘yan kallo a yau shi ne yadda babban ‘dan wasan Argentina Lionel Messi ke cikin matsin lamba, bisa rashin tabukawa kungiyar wani abin azo a gani.
KU KARANTA: Rasha 2018: Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles
Wanda hakan yasa da yawa daga cikin mutane ke ganin mutukar dan wasan bai tabuka rawar gani a wasan na yau ba, to tabbas karshensa a kungiyar yazo.
Da ma dai Messi ya taba ajiye rigarsa a shekara ta 2016, kafin daga bisani a roke shi ya dawo. Sannan an jiyo shi a watan Maris na 2018 yana cewa mutukar kasar tasu ta gaza cin kofin duniyar a wannan karon to karshen bugawa kasarsa tasa kwallo yazo.
To sai dai watakila kafin shi ya kai ga ajiye rigarsa da kansa, kasar Argentinar ma zata kore sa mutukar suka gaza samun nasara kan Najeriya a yau.
A hannu guda kuma, su ma 'yan wasan Nijeriyar sun daura damarar lallai-lallai zasu yi duk mai yiwuwa don ganin sun ragargaji Argentinar kamar yadda suka yiwa kasar Iceland.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng