Burina na gina coci-Inji wani shugaban yan fashi da makami bayan da ya shiga hannun hukuma
- Neman kudin gina coci ya sanya wani mutum shiga sana'ar fashi
- Abin takaicin shi ne har an kama shi bai tuba ba kuma bai gina cocinba
- Sai dai yayi nadamar shiga wannan mummunar harka
Wani dan shekaru 41 da haihuwa wanda ake zargi da yin fashi-da-makami mai suna Fidelis Nelso mai inkiya MP, ya ce ya shiga harkar fashi-da-makami ne domin ya tara kudin da zai bude coci nashi na kansa bayan da ya shiga hannun Jami'an yan sanda.
Ya bayyanawa Jaridar vanguard cewar ya dade da burin ganin ya gina coci, amma abun ya ci tura saboda matsalar rashin kudi da yake fama da ita, kuma wannan buri nasa ya dade da shi, shi yasa ya yanke hukuncin shiga wannan harka.
Nelson ya kuma shaidawa 'yan sanda cewa a 'yan kwanakin nan sai da suka yi fashin manya-manya har guda uku.
Hukumar 'yan sanda ta jihar Legas ta bayyanawa Jaridar vanguard cewa sun samu bayanai cewar akwai wasu yan fashi da zasu zo jihar ta Legas sayar da wasu kadarorin da suka kwato, shi yasa hukumar ta kasance cikin shiri kuma cikin nasara suka cafke su.
KU KARANTA: An tura Rundunar musamman zuwa Jihar Filato bayan barkewan rikicin Barkin Ladi
Bayan cafke su hukumar ta same su da mota kirar Toyota Camry, sai kuma yar karamar bindigar hannu da kuma layukan waya masu yawa. Shugaban tawagar yan fashin Nelso yace yana da yara har guda uku, kuma a halin da ake ciki yanzu haka matarsa bata san yana yin wanna sana'a ba.
Nelso ya ce "Ni ne wanda ya jawo Augustine cikin wannan harka saboda na duba naga Allah ya masa basira ta bangaren abinda ya shafi kida da waka, nayi hakan ne da zimmar ina gina coci mallakin kaina zan bashi bangaren kula da abinda ya shafi kida da waka".
Guda daga cikin wadanda aka kama mai suna Augustine wanda mawaki ne, ya bayyana cewa "Na hadu da Nelson ne a wani taro kuma ya nuna ya ji dadin yadda na nuna bajinta ta wajen kida da waka, har ya min alkawarin cewa zai shige min gaba don ganin na cika burina na zamowa mawakin addinin kirista.
"Daga bisani kuma sai yake fada min akwai wani aiki da zamu je wanda daga baya na gano fashi da makami ne, amma na nuna masa cewa ban taba yin hakan ba, amma sai dai ya rinjaye ni. Wannan shi ne mafarin shiga ta harkar fashi-da-makami".
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng