Atiku ya bayar da tallafin N10m ga wadanda guguwar iska ya cika da su a Bauchi
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayar da tallafin naira miliyan 10 ga mutanen da guguwar iska ya cika da su a jihar Bauchi.
A kwanan nan ne dai annobar guguwar iska ya cika da mutanen jihar Bauchi inda ya lalata dukiyoyi, gidaje, makarantu, wuraren kasuwanci, masallatai, da cocina.
Atiku ya bayar da wannan tallafi ne a ranar Litinin, yayinda ya ziyarci sarkin Bauchi, Rilwan Adamu a fadarsa.
Yace ya kai ziyara ne domin ya taya mutanen jihar da gwamnati alhinin annobar da ta afka masu kwanakin baya na guguwar iska da gobara a Bauchi da Azare.
KU KARANTA KUMA: Rasha 2018: Ba ma jin tsoron Messi – Super Eagles
Tsohon mataimakin shugaban kasar y ace zuwan sa Bauchi ya zo a kuraren lokaci ne saboda matsala da aka samu da jirgin da ya kamata ya kawo shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng