Rikicin Filato: Kasar Amurka ta tsoma baki kan kashe-kashen Jama’a

Rikicin Filato: Kasar Amurka ta tsoma baki kan kashe-kashen Jama’a

- Kasar Amurka tayi magana game da kashe-kashen da aka yi a Najeriya

- Mutane sama da 80 aka kashe a rikicin Barkin Ladi a cikin Jihar Filato

- Gwamnatin Kasar ta aikowa Najeriya jaje ta kuma nemi a dauki mataki

Kasar Amurka tayi magana game da rikicin da ke aukuwa a tsakiyar Najeriya inda ta nemi a dauki mataki. Kwanan nan ne wani rikici ya barke a Garin Barkin Ladi da ke cikin Jihar Filato.

Rikicin Filato: Kasar Amurka ta tsoma baki kan kashe-kashen Jama’a
Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo tare da Gwamna Lalong

Heather Nauert wanda wani babban Jami’i ne a Gwamnatin Kasar Amurka ya fitar da jawabi game da kashe-kashen da ya auku kwanan nan. Gwamnatin na Amurka tace dole a hukunta wadanda su ka aikata wannan danyen aiki.

KU KARANTA: Ana wata ga wata: 'Yan bindiga sun kashe wani Sarki

Hare-haren dai da aka kai sam ba su yi wa Gwamnatin Amurka dadi ba inda tayi kira da babban murya tana mai sukar lamarin da ake ta fama da shi a Arewacin Kasar. Amurka ta kuma yi wa al’ummar Yankin na Filato jaje.

Amurka ta nuna damuwan ta game da harin da ake kai wa a Yankin Arewa-maso-tsakiyan Najeriya da wasu sassa na Kasar. Kasar ta kuma yi kira ga Shugabanni su yi bakin kokarin na ganin kawo zaman lafiya a fadin Najeriya.

Nauert wanda shi ne ya fitar da wannan jawabi dai ya taya Shugaban Kasa Buhari takaicin abin da ya faru a Kasar sa. Shugaban Kasar dai tuni yayi Allah-wadai da wannan ta’adi ya kuma yi alkawarin magance matsalar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng