Wani Bawan Allah ya bayyana yadda ‘Yan Kabilar Birom su ka rika kashe Musulmai

Wani Bawan Allah ya bayyana yadda ‘Yan Kabilar Birom su ka rika kashe Musulmai

Wani Bawan Allah mai suna Chukwuka Jerri ya bada labarin yadda wasu Musulmai su ka sha da kyar a a hanya lokacin da rikicin Filato ya barke a karshen makon nan. Rikicin dai tsakanin Fulani da ‘Yan kabilar Birom yayi sanadiyyar mutuwar mutane da-dama.

Wani Bawan Allah ya bayyana yadda ‘Yan Kabilar Birom su ka rika kashe Musulmai

Rikici ya barke a Garin Barkin Ladi a Jihar Filato

Mista Jerri ta shafin sa na Tuwita mai suna MaziMum yace wani Abokin aikin sa da ya je rubuta wata jarrabawa a Garin Jos ya gamu da ha’ula’i a hanya inda wasu mutane su ka tare su a hanya su na binciken ko Musulmai ne su ko kuma Kiristoci.

Wannan mutumi yace Abokin na sa ya taki sa’a bayan da aka gano cewa duk Kiristoci ne a cikin Motar in ban da wata Mata guda kacal. Don dole dai wannan mata ta cire Hijabin ta gudun kar ayi mata yankan rago kamar yadda ake yi wa sauran Musulmai.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana masu hannu a cikin rikicin Filato

Bawan Allan yace a gaban sa aka rika fasa kan wasu Musulmai da ke dauke da kayan miya kamar kwallon kwa-kwa. Wasu matan dai sun sha ne don kurum an gan su dauke da jariri a baya amma da ta su ta kare kamar yadda wannan mutumi ya fada.

An dai kashe mutane fiye da 100 a Garin Barkin Ladi kamar yadda wannan Bawan Allah ya bayyana. Kun ji labari cewa dole dai jiya Gwamnatin Jihar ta sa dokar ta-baci domin kar rikicin tsakanin Fulani da ‘Yan kabilar Birom ya fi karfin hukuma.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya koka da ta’adin da aka yi a Garin na Filato inda yace kisan da aka yi bai yi masa dadi ba kuma abin Allah-wadai ne. Tuni ma dai Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya hau jirgi ya leka Yankin da abin ya faru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel