Assha: wani matsahi ya cakawa abokinsa wuka a ido

Assha: wani matsahi ya cakawa abokinsa wuka a ido

- Matsalar shaye-shaye da yawa take

- Wani aboki yayi cakawa abokinsa kwalba bayan da suka sha giya su kayi mankas

- Sai dai duk da tserewa da yayi 'yan sanda sun damko shi har an gurfanar da shi gaban kuliya

Rikici tsakanin wasu matasa da suke tsaka shan giyarsu a mashaya ya haddasa sanya guda halasar da ta kai ga ya cikawa dayan kwalba a ido.

Su dai mashayan biyu da ake musu kallo abokai suna cikin shan barasarsu ne kawai sai aka ji hayaniya ta barke tsakaninsu kan rabon wani kudi da ba’a san ko na menene ba.

Assha: wani matsahi ya cakawa abokinsa wuka a ido
Assha: wani matsahi ya cakawa abokinsa wuka a ido

Matashin da ake zargi da yin wannan aika-aikar, ya cakawa abokin nasa mai suna Alaba Akinleye kwalbar ne a idonsa na hagu. Amma ko da ya ga irin barnar da ya tafka nan da nan ya zurare ya arce, amma kuma tuni jami’an ‘yan sanda sun dana masa tarkon da akayi sana’a ya kama shi.

KU KARANTA: Wata mata ta roƙi kotu da ta umarci mijinta ya biya ta kuɗin kula masa da cikin sa

Yayin gurfanar da shi gaban kuliya a yau Litinin, dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa alkalin kotin majistire dake Badagry cewa, wanda ake zargin mai suna Abiodun Abayomi mai shekaru 22 ya aikata laifin ne tun a ranar 17 ga watan Yuni a yankin Badagry.

Kuma wannan laifi ne da ya saba da sashi na 171 na kundin manyan laifuka na jihar Legas na shekara ta 2011. A cewar dan sandan.

Amma sai dai wanda ake karar ya ce shifa bai ma sannan wannan maganar ba, a takaice dai shi bai aikata laifin komai ba.

Wannan ce ta sanya alkalin kotun mai shari’a Jimoh Adefioye bayar da belinsa kan kudi Naira dubu dari (N100, 000) sannan ya kawo wadanda zasu tsaya masa mutane biyu masu takardar shaidar biyan kudin haraji ga gwamnatin jihar ta Legas har na tsawon shekaru biyu.

Sannan ya daga sauraren karar zuwa 31 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng