Obasanjo ya maidawa Tinubu martani bayan ya caccake sa a taron APC

Obasanjo ya maidawa Tinubu martani bayan ya caccake sa a taron APC

A karshen makon nan ne mu ka samu labari cewa Jigon Jam’iyyar APC mai mulki na Kasa Asiwaju Bola Tinubu yayi kaca-kaca da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo. Sai dai wani na-kusa da tsohon Shugaban Kasar ya maida amsa.

Obasanjo ya maidawa Tinubu martani bayan ya caccake sa a taron APC

Obasanjo yayi wa Tinubu gorin neman goyon bayan sa a 2015

Tsohon Gwamnan Jihar Legas watau Asiwaju Bola Tinubu ya maida martani ne ga tsohon Shugaban Kasar nan Janar Olusegun Obasanjo na cewa ka da Shugaba Muhammadu Buhari yayi gigin tsaya takara a zabe mai zuwa na 2019.

KU KARANTA: PDP ta taya Oshiomhole murnar zama Shugaban Jam'iyyar APC

Babban jigon na Jam’iyyar APC Bola Tinubu yayi wannan jawabi ne a wajen gangamin APC inda ya kira tsohon Shugaban Kasar da rikakken mai murde zabe. Ko da dai Tinubu bai kama suna ba amma alamu sun nuna cewa da Obasanjo yake.

Bola Tinubu da yake magana a karshen taron na APC yace tsohon Shugaban Kasar bai da lasisin ba Shugaba Buhari shawara game da neman tazarce. Tinubu yace ya ma dai godewa Ubangiji da cewa ba Jam’iyyar su guda da tsohon Shugaban ba.

Sai dai wani Hadimin tsohon Shugaban Kasar ya maida martani ga Tinubu ta Jaridar Daily Trust inda yake cewa abin kunya ne ace irin su Tinubu da su ka nemi goyon-bayan Obasanjo domin ganin Buhari yayi nasara a 2015 su dawo su na wannan magana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel