Rikicin Plateau: Mutane sun fara kaura daga gidajensu

Rikicin Plateau: Mutane sun fara kaura daga gidajensu

- Mutanen jihar Plateau sun fara guduwa neman mafaka sakamkon barkewar rikici

- Kawo yanzu dai rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutane 86

Biyo bayan barkewar rikici a jihar Plateau yanzu haka mutane da yawa sun fara kaura suna barin gidajensu domin neman mafaka zuwa makwabtan kauyukansu da ake ganin kamar su da dan dama-dama.

Rikicin Plateau: mutane sun fara kaura daga gidajensu
Rikicin Plateau: mutane sun fara kaura daga gidajensu

‘Yan gudun hijirar da yawancinsu mata ne da yara kanana mazauna yankin Gashish a yau Litinin sun kauracewa gidajen nasu ne zuwa shelkwatar karamar hukumar Barkin Ladi sakamakon wani rikici da ya barke ranar Asabar. Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya rawaito.

Rikicin Plateau: mutane sun fara kaura daga gidajensu
Rikicin Plateau: mutane sun fara kaura daga gidajensu

‘Yan sanda sun tabbatar da cewa da fara rikicin kawo yanzu mutane 86 ne suka rasa rayukansu a dalilin harin da makiyaya suka kai yankin Gashish da Barkin Ladi, wanda yayi sandiyyar mutuwar mutane 6 da kuma raunata wasu da dama da harsashi da kuma saran adda.

KU KARANTA: Rikicin jihar Plateau: An sanya dokar ta baci a jihar Plateau

A yunkurin dakile watsuwar rikicin ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fitar dare a jiya a kananan hukumomi Barkin Ladi, Riyom da kuma Jos South.

Yanzu haka dai babban sufeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris ya dauki matakan gaggawa don ganin an shawo karshen matsalar bisa la’akari da a iya jiya kawai kusan mutane dari ne suka bakunci kiyama.

Rikicin Plateau: mutane sun fara kaura daga gidajensu
Rikicin Plateau: mutane sun fara kaura daga gidajensu

Sufeton ‘yan sandan ya aike da wasa rundunoni na musamman zuwa kananan hukumomin da abin ya shafa, sannan ya kuma sake aikawa da karin jirage biyu masu saukar ungulu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng