Ibtila’I ta fada ma mawakan Najeriya: An kashe guda, guda ya rasa yaronsa a ruwa

Ibtila’I ta fada ma mawakan Najeriya: An kashe guda, guda ya rasa yaronsa a ruwa

Wani matashin mawakin gambara dan Najeriya mai shekaru 15, Jordan Gbolade Jaiyeola ya gamu da ajalinsa a hannun wasu gungun matasa da suka fasa wani taron biki da aka shirya ma kananan yara a birnin Landan, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan ibtila’I ta fada ma Jordan ne a daidai lokacin da yan daban suka far ma kusan yara dari biyu da suka halarci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar abokinsu da ya gudana a anar Asabar din data gabata, a daidai lokacin da suke fita daga wajen bikin.

KU KARANTA: Karyar karatu: Jami’an yaki da rashawa sun yi ram da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha

Ibtila’I ta fada ma mawakan Najeriya: An kashe guda, guda ya rasu yaronsa a ruwa
Jordan

A daidai wannan lokaci ne matasan suka kaddamar da harin mai kan uwa da wabi, inda suka caccaka ma Jordan wuka, nan take ya fadi matacce, inda aka jiyo abokansa suna kuwwar an kashe shi.

Daga bisani jami’an Yansandan birnin Landan sun garzayawa inda lamarin ya auku, inda suka tsinci karo da gawar Jordan kwance male male cikin jin.

Sai dai dayake Hausawa na cewa idan an bi ta barawo, abi ta masi sawu, rahotanni sun tabbatar da cewa Jordan ya fito a cikin wasu wakoki da aka watsa a shafin Youtube, dake rura rikicin kungiyoyin yan daba.

Wata daga cikin mahalarta bikin, Ellie ta bayyana cewa: “Na ji muryar yara guda uku haka suna ihu, kuma naga gawarsa kwance, haka zalika na hangi ma’aikatan ceton rai suna ta kokarin ceto rayuwarsa, daga bisani suka rufe shi da wani zani.”

A wani labarin kuma, diyan fitaccen mawakin Najeriya, D’banj ya gamu da mummunan rashi na mutuwar dansa, Daniel Oyebanjo III, sakamakon nutsewa da yayi a cikin kwamin ruwan gidansu, a yayin da matarsa ke cikin gida, shi kuma yana kasar Amurka ya halarci bikin karramawa na BET a Amurka.

Ibtila’I ta fada ma mawakan Najeriya: An kashe guda, guda ya rasu yaronsa a ruwa
Yaron Dbanj

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel