Gasar cin kofin Duniya: Muna shakkar Ahmad Musa – Inji Ajantina

Gasar cin kofin Duniya: Muna shakkar Ahmad Musa – Inji Ajantina

Wasu yan kasar Ajantina dake mara ma kungiyar kwallon kafar kasarsu baya sun bayyana dan wasan Super Eagles Ahmed Musa a matsayin babbar barazanar dai basu matsala a wasan da kasashen biyu zasu fafata a ranar 26 ga watan Yuni a cigaba da gasar cin kofin Duniya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito guda daga cikinsu mai suna Santiago Lautaro yana bayyana ra’ayin cewa yan wasan Najeriya sun fi hadin kai da sanin junansu akan yan wasan kasar Ajantina, don haka yake ganin da kamar wuya Ajantina ta ci Najeriya.

KU KARANTA: Gardawa 4 sun Lakada ma Mijin yar uwarsu duka har lahira, sakamakon cutarta da yake yi

“Mu dai kam muna da yan wasa masu suna, amma basa fahimci juna ba a kwallace, Ahmed Musa babban barazana ne, kamar yadda Messi yake, sai dai kasan yafi Messi kokari a wannan gasar.” Inji shi.

Gasar cin kofin Duniya: Muna shakkar Ahmad Musa – Inji Ajantina
Ahmed Musa

Shi kuwa Matias Franco cewa yayi ya san Ahmed Musa yana da sa’an cin kasar Ajantina, “Amma bana fatan ya samu nasara akanmu, duk da dai bama wani kwallon kirki, don gaskiya bai kamata mu koma gida tun yanzu ba.”

Daga karshe, wani mai suna Augustin Nicolas ya baiwa kansa kwarin gwiwar Ajantin zata lallasa Najeriya a ranar Talata, a wasan da zasu buga a babban birnin kasar Rasha, St Petersburg.

Haduwar Najeriya da Ajantina a ranar Talata zai zamo wasa na hudu da kasashen biyu ke haduwa a gasar cin kofin Duniya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng