Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun hallaka daliban jami’a 2 sannan sun sace 1 a jihar Katsina

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun hallaka daliban jami’a 2 sannan sun sace 1 a jihar Katsina

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Bagiwa dakekaramar hukumar Mani, jihar Katsina sannan sun kashe daliban jami’a guda biyu.

Maharan sun kuma jikkata mutum daya tare da sace wani, dukkansu daliban jami’ar Al-Qalam dake Katsina ne.

Wadanda aka kashe sune Ibrahim Bature, dan shekara 22 yana mataki na 400, da Rabi’u Abubakar dan shekara 22 yana mataki na 200.

Wani kakakin ahlin daliban, Alhaji Lawal Bagiwa ya fadama kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Bagiwa cewa yan bindigan sun kuma harbi mahaifiyar yaran sannan suka sace bbban yayansu, Umar.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun hallaka daliban jami’a 2 sannan sun sace 1 a jihar Katsina
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun hallaka daliban jami’a 2 sannan sun sace 1 a jihar Katsina

Ya kara da cewa yan bindigan da suka kai mamaya kauyen da misalin karfe 1:15 na tsakar daren ranar Lahadi, sun kai hari gidan yanuwansu, suna ta harbi ba tare da sun bukaci komai ba.

Bagiwa ya bayyana cewa tunda yan bindigan suka tafi da dan uwansu basu ji daga gare su ba.

Ya bayyana cewa har yanzu iyalan basu san dalilin kisan da sacewar ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu kaiwa yan Boko Haram mai

Bagiwa ya bayyana cewa rundunar yan sandan jihar Katsina sun ziyarci gidan sun kuma yi alkawari kwato wanda aka sace.

Kakakin yan sandan, SP Isah Gambo wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana cewa yan sanda na bincikar lamarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng