Akwai yiwuwar Mikel Obi ba zai buga wasan gobe ba na Najeriya da Argentina

Akwai yiwuwar Mikel Obi ba zai buga wasan gobe ba na Najeriya da Argentina

Kungiyar likitocin 'yan wasan kwallon kafa na Super Eagles da suke wakiltar Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da yake wakana a kasar Rasha, suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa Mikel Obi ya samu cikakkiyar lafiyar da zai samu damar buga wasan da Najeriya zata yi da kasar Argentina a gobe Talata

Akwai yiwuwar Mikel Obi ba zai buga wasan gobe ba na Najeriya da Argentina

Akwai yiwuwar Mikel Obi ba zai buga wasan gobe ba na Najeriya da Argentina

Kungiyar likitocin 'yan wasan kwallon kafa na Super Eagles da suke wakiltar Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da yake wakana a kasar Rasha, suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa Mikel Obi ya samu cikakkiyar lafiyar da zai samu damar buga wasan da Najeriya zata yi da kasar Argentina a gobe Talata.

DUBA WANNAN: An kashe Fulani 32 a wani rikicin kabilanci

A binciken da likitocin suka gabatar ya nuna cewa, dan wasan ya samu karamin rauni a hannunsa a dai-dai lokacin da ake gab da tashi daga wasan da Najeriya ta buga da kasar Iceland inda Najeriya ta lashe wasan da ci 2 a ranar juma'ar nan.

Duk da dai mai horasa da 'yan wasan na Super Eagles, Gernot Rohr yana kallon ciwon a matsayin karami wanda kuma yake ganin ba zai hana dan wasan buga wasan da kasar ta Argentina ba.

Rohr ya kuma nemi 'yan wasan da su dinga kokarin dukan kwallo a duk lokacin da suka ga kwallon a dab da ragar Argentina.

Rohr ya bayyana cewa, wasan da za'ayi na gobe zai kasance mai zafi, kuma zasu yi iya bakin kokarin su domin ganin sun samu nasara akan Argentina din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel