An kashe mutane 3, sannan an sace matar sarki a wata jiha a Najeriya

An kashe mutane 3, sannan an sace matar sarki a wata jiha a Najeriya

Jami'an hukumar 'yan sanda na jihar Ondo sun tabbatar da kisan mutane 3 a garin Oba Ile, dake karamar hukumar Akure babban birnin jihar Ondo a wannan karshen makon

An kashe mutane 3, sannan an sace matar sarki a wata jiha a Najeriya

An kashe mutane 3, sannan an sace matar sarki a wata jiha a Najeriya

Jami'an hukumar 'yan sanda na jihar Ondo sun tabbatar da kisan mutane 3 a garin Oba Ile, dake karamar hukumar Akure babban birnin jihar Ondo a wannan karshen makon. Sannan hukumar 'Yan sandan sun tabbatar da sace matar wani sarkin gargajiya dake garin Auga Akoko.

DUBA WANNAN: In kana duniya kasha kallo: An gano wani kashin kunkuru mai shekaru miliyan 150 a duniya

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan na jihar Ondo, Femi Joseph ya sanarwa da majiyar mu Legit.ng cewa lamarin ya farune a ranar juma'a da asabar a wurare daban daban.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa mazauna gurin suna cikin tsoro a cikin ranakun karshen makon saboda yanda suka ga mutane na faman mutuwa a yankin.

Bayan haka kuma mun samu labarin cewar anyi garkuwa da matar wani sarkin gargajiya dake yankin. Anyi garkuwa da Sarauniya Olukemi Agunloye, tare da direban ta a tsakanin Auga da Ise Akoko.

Sarkin, Oba Samuel Agunloye yace suna hanyar su ta zuwa Ugbe ne lokacin da abun mara dadin ji ya faru.

Yace wayoyin su duk a kashe tun daga lokacin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel