Anfani a juji: Anfani 5 da bakin gawayi ke yi a rayuwar bil'adama
Ko shakka babu bakin gawayi na daya daga cikin abubuwa masu matukar anfani da mutane kan banzatar a rayuwar su watakila saboda rashin sani ko jahiltar alfanun da Allah ya tattara a tare da shi.
Hakan ne ma ya sanya Legit.ng ta dukufa wajen zakulo maku kadan daga cikin alfanun na sa a rayuwar bil'adama.
KU KARANTA: Musulunci zai mamaye Najeriya nan da 2043
Fatan mu shi ne daga yau za mu waiwaye shi domin yin anfani da shi a rayuwar mu ta yau da kullum.
1. Maganin wari: Masana sun tabbatar da cewa bakin gawayi yakan zuke dukkan wani irin nau'in wari a duk inda yake.
2. Gawayi na hana lalacewar abinci: Bincike ya tabbatar da cewa dukkan abincin da aka sawa ruwan gawani to ba zai taba lalacewa ba.
3. Wankin hakora: Tamkar mangoge baki na zamani ko ma fiye da hakan, bincike ya tabbatar da cewa gawayi yana wanke hakora fes-fes.
4. Kwaranye guba: Idan kana kokwanton abinci yana tare da irin maganin nan na kwari ko guba dake da lahani a jikin dan adam, gawayi yana wanke ta.
5. Saurin warkar da ciwo: Haka zalika bincike ma ya tabbatar da cewa gawayi yakan taimaka wajen saurin warkewar ciwo.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng