Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya

Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya

- "Soyayya rayuwa ce wani sa'in ta kan zamo hadari" wasu

- An sha yin tambayar shin zai yiwu kuwa samari da 'yan mata suyi soyayya babu karya a ciki amma sai dai amsar da take biyo har yau bata gamsar ba

Yanzu dai ƙarya ta zama ruwan dare a soyayya tsakanin samari da yan mata, sai dai akwai wasu ƙaryayyaki da suka fi shahara a bangaren samari, hakan ba yana nufin yan matan ba sa yin karya ba, su ma da akwai nasu irin salon ƙaryar, sai dai a nan za a yi duba ne akan wasu kadan da samari ke shararawa yan matan.

Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya
Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya

1- Ke kaɗai nake muradi a rayuwa:

Sau da yawa zaka ji samari na fadawa mace cewa ita kadai suke muradi a rayuwa, amma da zaka yi duba sosai akan wanda ya furta wannan lafazi zaka same shi da jerin-gwanon yan mata daban-daban wanda suma hakan yake fada musu. Kadan ne cikin samari zaka same su wanda in har suka furta hakan yake tabbas daga zuciyar su.

Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya
Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya

2- Ke kaɗai ce, bani da Budurwa

Wannan ma wani salon karya, sau da dama zaka riske saurayi ya fadawa budurwa haka ne saboda ya samu karbuwa a wajenta, amma maganar gaskiya ba haka zancen yake ba, saboda zaka iya samun sa da yan mata da yawa a lokaci daya. Wannan salo na karya shi ma ya yi fice a tsakanin samari da yan matan baki daya.

Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya
Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya

3- Gaba daya dangi na sun san da zamanki

Allah sarki yan mata, saurayi sai ya dage ya shararo miki karyar cewa danginsa da mahaifiyarsa ta san dake a matsayin wadda yake so. In har haka ne abinda ya fada ya kamata ace ko sau daya ne ya kai ki wajen mahaifiyar tasa kun gaisa ko kuma ya hada ku ta waya kuke gaisawa ko kuma ya hada ki da 'yan uwansa kuke yin zumunci wanda hakan ne zai tabbatar miki da gaskiyar abinda yake fada.

KU KARANTA: Cin fuska ko yabawa: An baiwa dalibin da ya zamo zakara a jami’a kyautar Naira dubu biyu

4- Abokiyar aiki na ce

Zaki iya samun saurayi tare da wata daban amma idan kin yi magana sai ya ce miki abokiyar aikinsa ce, ma'ana suna aiki tare ne a wajen aikinsa, amma da zaki yi bincike na tsanaki zaki riske cewar budurwarsa ce. Wannan nau'i na karya shi ma ya yi shuhura sosai a tsakanin samari.

5- Ke kaɗai ce a rayuwata

Allah ya tsari gatari da saran shuka, ya kamata dai samari su rage yiwa yan mata karya, dalili kuwa a nan shi ne duk saurayi da ya fada miki haka, to, tabbas ki sake tamabayar sa shin hakan da gaske domin ki samu tabbaci.

Don da yawansu zasu fada miki haka amma zaki same shi ba wai ke kadai yake soyayya dake ba watakila ma har ƙawarki ko aminiyarki yake soyayya da ita ba tare da sanin ki ba.

Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya
Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng