Aikin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara, Soji sun ara sako bayanai

Aikin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara, Soji sun ara sako bayanai

- An kaddamar da shirin Operation Idon Raini a jihar

- Kashe-kashen zun fara sauki yanzu

- An kashe akalla 30 a dazu, an kuma kama makamansu

Aikin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara, Soji sun ara sako bayanai

Aikin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara, Soji sun ara sako bayanai

Sanarwar da Kanar Muhammad Dole na dibishin 1 ta sojin Najeriya da aka kai jihar Zamfaraa, ta fitar da sanarwa ta hannun Janar SK Sheka, inda take albishir da kai harin sunkuru kan zaliman 'yan bindiga da ke kai hari kan jama'a a yankunan Gusau da kewaye.

A kauyen jan-birni, dake karamar hukumar Maru, da asubahin yau asabar, sojin sun sami nasarar kai hari a makwantar ja'iran a inda suke kaa sansanoninsu bayan kai hari.

A takaice dai, an kama ukku daga barayin, an kashe 20, saura kuma sun tsere, wasunsu da harbin harsashii a jikunansu.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta dauki mata masu duba hadurra aiki saboda mata zasu fara tuki

Hukumar na kara kira ga jama'a dasu ci gaba da kawo bayanai na makwantar muggan, da ma wasu motsi da basu ganewa ba.

Shi kansa wannan hari an sami bayanan sirri ne daga mutan gari, inda suka kawo labarin maboyar muggan.

An kama bindigogi 5 AK da pistol, da biyu na gargajiya, harsasai, wayoyi, kudade, sai wukake da sauran kayan mugunta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel