Wasan Najeriya, Maradona, tsohon dan ball, kuma tsohon kwach, yayo kashedi kafin wasan Najeriya

Wasan Najeriya, Maradona, tsohon dan ball, kuma tsohon kwach, yayo kashedi kafin wasan Najeriya

- Wasan Najeriya da Argentina zai zo nan da kwanaki ukku kacal a Talata

- Diego Maradona ya ja kunnen coach din Argentina, Jorge Sampoli da ya kara kaimi a wasan kofin duniya ko kuma kada ya dawo Argentina

- Maradona ya fusata da abinda ya gani, wanda yace sakamakon rashin shirin kasar shi ne wanda ya jawo yin kunnen doki da kasar Iceland

Wasan Najeriya, Maradona, tsohon dan ball, kuma tsohon kwach, yayo kashedi kafin wasan Najeriya
Wasan Najeriya, Maradona, tsohon dan ball, kuma tsohon kwach, yayo kashedi kafin wasan Najeriya

Diego Maradona ya ja kunnen coach din Argentina, Jorge Sampoli da ya kara kaimi a wasan kofin duniya ko kuma kada ya dawo Argentina.

Maradona ya fusata da abinda ya gani, wanda yace sakamakon rashin shirin kasar shi ne wanda ya jawo yin kunnen doki da kasar Iceland.

Diego Maradona ya yanke shawarar coach Jorge Sampoli ya nemi wata kasar in dai suka cigaba da irin wannan wasan a gasar kwallon kafar.

Jarumin gasar kwallon kafar na shekara na 1986 ya damu da wasan da yaga yan kasar shi sun buga kuma bai yi kasa a guiwa ba gurin nuna bacin ranshi akan wasan da Sampaoli da sauran yan wasan suka buga a Moscow.

Maradona yace laifin yin kunnen dokin ya rataya a wuyan tsohon Chile da coach Sevilla, wanda ya taba fuskantar kalubale daga mutumin da ya kai Argentina kwata final a shekarar 2010.

DUBA WANNAN:

"Tsarin wasan shi abin kunya ne, ban ga laifin yan wasan ba. Na fi dora laifin akan rashin shiri, wanda kiri kiri munsan basu shirya ba." Inji Maradona.

"Lokacin maganganu ya wuce, zaku iya zuwa da coach 25, amma fa sai kunyi aiki- munga Iceland sun kokarta fiye da Argentina kuma wannan abin ya bata min rai sosai."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng