An dauki sabbin mata aikin kula da hadurra yayin da matan Saudiyya suka fara tuqa mota

An dauki sabbin mata aikin kula da hadurra yayin da matan Saudiyya suka fara tuqa mota

- An hana mata tuqa mota a Saudiyya tsawon shekaru a karkashin sharia

- Maluman Islama ne suka hana wai tukin zai kawo yawon zinace-zinace

- Yariman Saudiyya ya kwatowa matan 'yancinsu na yin yadda suke so

An dauki sabbin mata aikin kula da hadurra yayin da matan Saudiyya suka fara tuqa mota
An dauki sabbin mata aikin kula da hadurra yayin da matan Saudiyya suka fara tuqa mota

A gobe Lahadi ne, ake sa rai matan Saudiyya, wadanda sune kadai suka rage a jerin matan duniya wajen samun yancin yin yadda suke so da rayuwarsu, saboda takunkumai da karfa-karfa da maza da malamai suka qaqaba musu karkashin sharia'r Islama tsawon shekaru.

Sai dai 'yancin da zasu samu zai zo da sabon naqasu, ganin wannan karon, ba 'yancin cire hijabi ko iya fita babu dan rakiya bane, ba kuma iya zuwa silima ko sitadiya bane, wannan 'yancin tuka mota ne.

Ana horar da jeri na farko na mata masu duba hadurran motoci don taimako ga direbobi mata a kasar Saudi Arabia.

Rahoton yace za a ba mata damar tuki a daular musuluncin a ranar lahadi bayan haramta tukin mata da akayi a karni aru aru da suka gabata.

Mata arba'in ne kamfanin inshora Najm tayi haya don murnar a babban birnin Riyadh. Dukkaninsu sun sanya abaya, wasun su ma da niqab.

Duk da dai ba a san takamaiman lokacin da matan zasu fara aikin su ba kuma ta yaya zasu fara a cikin kasar mai tsauraran matakai na hana mata mu'amala da mazan da ba muharraman su ba.

Sakamakon canje canje da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman yake kawo wa, tare da burin bunkasa tattalin arzikin su don dena dogaro akan man fetur, suna kawo canje canje a al'adun kasar. Inda matasan kasar ke maraba da sauye sauyen, amma wasu daga cikin yan kasar na tsoron sauyin zai iya taba addini.

Lokacin da Shugaba Salman ya zartar da kawo karshen haramcin tukin matan, ya ba wa Gwamnatin wa'adin wata tara don su shirya gabatar da mata direbobi akan titin kasar.

Ministan cikin gida na kasar Saudi Arabia dai yana ta shirye shirye, ta hanyar Bude gidajen koyon tukin motoci kuma da Bude guraren samar da lasisi na tukin mata.

Koyon mota da tuka ta dai, ga ma wanda ya iya, sai da la-haula, sai an kula, sannan sai an jure da hakuri, wannan kuwa ko mace ko namiji dole a ga wallar mutum muddin yanzu ya fara.

DUBA WANNAN: Jiga-jigan APC na kacamiya kan kujerun takara a Abuja

Matan, zasu bazama tituna domin more mota yadda mazan kasar keyi, wanda ya hada da tuki, ribas, parking da ma zuwa unguwa, sai dai an hana matan barin gari don bulaguro ba tare da namiji ba, ko da kuwa macen ta balaga ko ta haifa.

Gwamnati ta dauki hayar masu kula da kiyaye hadurra da bin kadin hadari, birni-birni, don gujewa kwamacalar 'yan koyo, wadanda suka amshi lasisin su don bazama tuki a gobe lahadi.

Sai muce, A hau lafiya a sauko lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng